Akwai jan aiki a gaban Messi a wasansu da Bayern

    0

    © 2020 Copyright RFI – An adana duk haƙƙoƙi. Ba ruwan RFI da labaran da suka fito daga shafukan waje. Yanayin masu saurare daga ACPM/OJD.

    Akwai jan aiki a gaban Lionel Messi na Barcelona dangane da samar wa kungiyarsa gurbi a matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai.

    A gobe Juma’a ne Barcelona za ta kece raini da Bayern Munich a Lisbon, wasan da ake kallo a matsayin karan-batta, lura da cewa, kungiyoyin biyu na rike da kambin gasar zakarun Turai har guda biyar-biyar kowacce daga cikinsu.

    Kofin La Liga ya subuce wa Barcelona, bayan Real Madrid ta dage kofin a bana, yayin da a yanzu kungiyar ke hararar kofin zakarun Turai.

    Barcelona ta dogara kacokan kan Messi mai shekaru 33 a wasan da za ta yi da Bayern Munich wadda ba kanwar-lasa ba ce.

    Kodayake Messi ya jefa kwallaye biyu a wasan da Barcelona ta doke Bayern Munich a shekarar 2009 a matakin kwata fainal a gasar zakarun Turai, inda a wanan lokacin ma, Barcelona ta lashe kofin gasar karkashin jagorancin Pep Guardiola.



    SOURCE: https://www.w24news.com

    Donnez votre avis et abonnez-vous pour plus d’infos

    Vidéo du jour:

    Laisser un commentaire